IQNA

Daesh ta Dauki Nauyin Harin Ta'addancin Zainabiyyah

23:52 - June 11, 2016
Lambar Labari: 3480504
Bangaren kasa da kasa, kungiyar ta'addanci ta Daesh ta dauki nauyin harin ta'addancin da a aka kai a yankin zainabiyya da ke kusa d birnin Damascu na Syria.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Uyunul khalij cewa, kungiyar ta'addanci ta Daesh ta dauki nauyin harin ta'addancin da a aka kai a yankin zainabiyya da ke kusa d birnin Damascu a yau.

An kai hari biyu ne, a yankin Husainiya daya kuma a yankin Al-tin dukakninsu yankuna ne biyu da suke cikin unguwar ta Zainabiyyah, inda mutane 20 suka rasa rayukansu da suka hada da 13 mutanen gari, sai kuma jami'an tsaro 7.

Wannan dai bas hi ne karon farko da yan ta'addan da suke samun dauki da taimako daga kasashen larabawa suke kaddamar da harin ta'addanci a kan wannan yanki ba, wanda ke da cunkoson jama'a masu ziyara.

A bangaren guda kuma yan ta'addan sun harba makaman roka a kan yankin Zahra wanda na mabiya mazhabar shi'a na kasar ta Syria, inda a nan ma mutane fararen hula da dama suka samu raunuka.

Kasashen larabawan yankin tekunfasha ne dai suka kafa kuma suke daukar nauyin kungiyar ta ta'addanci ta daesh da sauran kungiyoyin da suke gudanr da irin wadannan ayyuka.

3506007

captcha