
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga karamin ofishin jakadancin kasar Irana Ghana cewa, Sheikh Abdulmumin wanda malami ne na mazhabar shi’a, yana gudanar da wannan tafsiri a kowace shekara alokacin azumi.
Wannan tafsiri dai ana gudanar da shi ne a masallacin Ahlul-bait (AS) a garin Tamale da ke arewacin kasar, inda mutane da dama suke halarta kuma suke sauraren abin da yake fada.
Masu halaratr wanann zaman tafsiri dai sun hada da mabiya mazhabar shi’a da kuma sauran musulmi masu sha’awar jin wa’azin malamin.
Za a ci gaba da gudanar da wannan zaman tafsirin kur’ani mai tsarki da wannan malamin yake gudanar daga nan har zuwa karshen wanann wata na Ramadan a mai alfarma.