
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na radioalgerie cewa, Tun kwanaki biyu da suka gabata aka fara gudanar da gasar kur’ani mai taken Tajul Kur’an a kasar Aljeria a birnin Algiers fadar mulkin kasar a karo na shida.
Wannan gasa dai ana gudanar da ita ne a mataki na kasa baki daya, kamar yadda kuma kowa yana da damar da zai iya shiga cikinta matukar dai ya cika sharuddan da ake bukata na shiga gasar.
An bude gasar ne tare da halartar Muhammad Isa mnista mai kula da harkokin addini akasar, sai kuma Hamid Qarin ministan sadarwa na kasar, sai kuma Taufiq Khallad babban darakta na hukumar radio da talabijin na kasa baki daya.
Wannan gasa wadda take mayar da muhimamnci ga bangaren karatu da salon tartili da kuma tajwidi, ana gdanar da ita ne a cikin azumi, kuma a wurin ne ake bayan da buda baki ga mahalrta.
A wanann karon wadanda suka kai ga mataki na karshe da za su kara domin fitar da na daya su ne Ruzqi Maddah daga yankin Sutaif, sai kuma Hannan Mushri daga yankin Tabsa, wadan za su kara amatakin karshe domin fitar da na daya.
Haka nan kuma bisa ga al’ada ana gudanar da wannan gasar ne tare da watsa ta kai tsaye a gidan talabijin na kasar.
Dukannin bangarorin da ake gudanar da gasar za su kamala fitar da wadanda za su suje mataki na karshe, kuma karshen watan Ramadan ne za a fitar da mutane takwas wadanda a cikinsu ne a fitar da mataki na uku da na biyu da kuma na daya.