IQNA

An Yi Kira Ga Kiristocin Da Musulmin Najeriya Su Gaba Da Zaman

23:51 - June 12, 2016
Lambar Labari: 3480508
Bangaren kasa da kasa, majalisar malaman addinin muslnci a jahar Osun ta kirayi kungiyar CAN ta mabiya addinin kirista da su kara bayar da hadin kai domin ci gaban zaman lafiya a tsakaninsu da musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar DAILY Trust cewam Alhaji Mustafa Alwiya mataimakin shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta jahar Osun, yay i kira ga mabiya addinin kirista da su ci gaba da bayar da hadin kai domin zaman lafiya tsakaninsu da musulmi a jahar.

Wannan kira ya zo sakamakon yadda wasu daga mabiya addinin kirista ajahar suka nuna damuwa dangane da batun saka hijiabin muslunci da mata musulmi suke yi, wanda suke dnganta hakan da barazana ta tsaro, musamman kan batun Boko Haram.

Tun a lokutan baya ne shugaban kasar ya bayyana cewa idan dai har ta kama za a iya hana saka hijabi saboda matsala ta tsaro, idan dai har da bukatan hakan, wanda wasu suke fakewa da hakan domin neman a hana sa hijabin, duk kuwa da cewa a hukumance dai ba a hana hakan nea Najeriya ba.

3506320

captcha