
Kamfaninin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da bukin rufe babban taron gasar ne a birnin Dakar fadar mulkin kasar ta Senegal, tare da halartar wasu daga cikin jami'an gwamnatin kasar, da kuma jakadun kasashen muuslmi mazauna birnin.
Wannan gasar kur'ani ta kasar Senegal dai ita ce mafi girma da ake gudanarwa a cikin kasashen yammacin Afirka, inda makaranta da mahardata daga dukkanin sassa na kasar suke haduwa abirnin Dakar domin gudanar da gasa a dukkanin bangarori, na karatu, harda, da kuma tajwidin karatun kur'ani mai tsarki.
Akasarin masu halartar gasar dai mabiya darikokin sufaye ne, da suka hada da Tijjaniya, Muridiyya da sauransu, kamar yadda kuma manyan shehunnai da masana na kasar sukan halrci wurin.
Daga cikin jami'an diplomasiyya da suka halarta kuwa Ainullah Qashqawi jakadn Iran da kuma Sayyid Hassan Esmati shugaban ofishin kula da harkokin al'adu a kasar.