
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya ahbarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar muslunci ta kasar Birtaniya cewa, wannan gasa an fara gudanar da ita tare da halartar dalibai na makarantun kur'ani na musulmi.
An kasa gasar zuwa gida uku, da ya hada da bangaren harda, karatu da kuma tajwidi.
Kamar yadda kuma aka kasa masu gasar da kuma juzuin da za su yi gasa, wasu daga na daya zuwa na biyu har dai zuwa, bakwai da goma.
Wadanda za su gudanar da gasa a cikin surat waki'a masu kasa da shekaru 15 ne, wadanda kuma shekarunsu suka haura hakn za su gasar a daga surat Rahman.
Haka nan kuma akwai bangaren kira ta tartili wadda za ta hada bangarorin mata da kuma maza.
Sai kuma akwai bangaren amsa tambayoyi da suka shafi ma'anoni na ayoyin kur'ani da ake karantawa domin sanin karfin fahimta da kuma tafsirin mai gasa.
Babbar manufar wanann gasa dai it ace karfafa matasa musulmi mazauna kasar ta Birtaniya kan harkokin kur'ani mai tsarki, da kuma kara basu karfin gwiwa kan lamarin addini da yi msuu saiti.
Za a ci gaba da gudanar da ita har zuwa karshe wannan wata na azumi mai alfarma.