IQNA

A Gobe Ne Za A Rufe Gasar Kur’ani Ta Turkiya

19:14 - June 16, 2016
Lambar Labari: 3480519
Bangaren kasa da kasa, a gobre ake rufe gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da ake gudanarwa a masallacin Fateh a Istanbul a kasar Turkiya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a gobene idan Allah ya kai mu da kimanin karfe 14 na yamma za a fara gudanar da taron rufe gasar a masallacin Fateh na Istanbul.

Kwamitin shirya gasar dai ya bayyana sunayen wasu daga cikin alkalan wadanda su ne za su bayyana mutanen da sukanuna kwazo a dukkanin bangarorin gasar, indsa za a zabi mutane na daya na biyu da kuma na uku.

Mahdi Gholam Nejad da Saed Ali Akbari suna daga cikin wadanda ska wakilci Iran a wannan gasa, kuma dukkaninsu sun kai ga mataki na karshe a cikin gasar.

A yau ne dai ake gudanar da mataki na karshe wannan gasa, wanda kuma daga cikin suka ki g wannan mtaki za afitar da wadnda za su lashe gasar.

3507628

captcha