
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga tashar talabijin ta Press TV ta bayar da rahoton cewa, kotun masarautar kasar ta Bahrain ce ta bayar da bayar da umarni ga jami'an 'yan sanda da suka kai farmaki kan babban ofishin jam'iyyar da ke birnin Manama ba tare da sanar da 'ya'yan jam'iyyar ba ko kuma ba su notis, inda 'yan sandan masarautar ta Bahrain suka afka kan ofishin tare da cin zarafin jama'a da ke wurin, kwashe kaddarorin jam'iyyar, tare da garkame ofishin.
Wannan mataki dai ya fuskanci kakkausar suka daga bangarori daban-daban na duniya, da hakan ya hada da majalisar dinkin duniya da kuma wasu daga cikin kasashen turai, musamamn gwamnatin kasar Switzerland, wanda ta bayyana hakan a matsayin wani aiki na cin zarafin 'yan adam da kuma yi musu mulkin kama karya.
Kafin wannan lokacin dai mahukuntan kasar sun kame babban sakataren jam'iyyar ta Alwifaq Sheikh Ali salman, tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru hudu a gidan kaso, kafin daga bisani kuma suka mayar da hukuncin daurin shekaru tara a gidan kaso
A daya bangaren sojojin kasar Bahrain sun kame Nabil Rajab Na Kungiyar Kare Hakkokin Bil'adama.
Mai dakin mutumin da aka kame, Sumayyah Rajab, ta buga a shafinta na Internet cewa; Sojojin sun shiga sun kan karai, kuma sun yi awon gaba da mai dakinta.
Shi dai Nabil Rajabi yana daga cikin kusoshin jam'iyyun hamayyar kasar, wanda a baya ma dai an sha kamashi.
Makwanni biyu da su ka gabata mahukunta a kasar ta Bahrain sun daure Sheikh Ali Salman zaman kurkuku na shekaru 8.
Shekaru kusan 5 kenan da al'ummar kasar su ka yunkura da zummar kawo sauye-sauyen siyasa a cikin kasar, sai dai mahukunta sun yi amfani da karfi wajen murkushe su.