Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalt daga
alalam cewa a cikin wannan makon ne kotun masarautar Bahrain ta sanar da
haramta jam'iyyar Alwifaq, jam'iyyar siyasa mafi girma a cikin dukkanin
kasashenlarabawa na yankin tekun fasha, wadda fiye da rabin mutanen kasar ta
Bahrain suke goyon bayanta, inda jami'an tsaro a cikin kayan sarki suka
kaddamar da farmaki a kan babban ofishin jam'iyyar da ke Manana fadar mulkin
kasar, suka ci zarafin dukkanin mutanen da suka samu a wurin, suka kuma sace
muhimman kaddarori na jam'iyyar da suke a cikin ofishin, kafin daga bisani kuma
suka rufe wurin baki daya suka tafi da makullan.
Kafin daukar wannan mataki da 'yan kwanaki, kotun masarautar ta kara tsawon wa'adin daurin da ta yi wa babban sakataren jam'iyyar Sheikh Ali Salman, inda a baya ta sanar da daure shi shekaru hudu a gidan kaso, amma a cikin 'yan kwanakin da suka gabata ta sanar da mayar da hukuncin zuwa daurin shekaru 9 a gidan kaso, bisa zarginsa da yin kalamai na sukar salon siyasar wannan masarauta.
A cikin kasa da sa'oi arba'in da takwas da suka gabata, jami'an tsaron masarautar Bahrain sun kira yi manyan malaman addini da limaman Juma'a na mabiya mazhabar shi'a a kasar, inda suka ja kunnensu dangane da gudanar da salla ko sauran ayyuka na ibada sabanin mahangar masarautar, tare da hana su yin magana a kan dukkanin abin da ya shafi batu na siyasa ko salon mulki a kasar.
Kimanin kashi 86% na al'ummar kasar Bahrain dai mabiya mazhabar shi'a ne, amma kuma masarautar da ke mulki a kasar wadda 'yan mulkin mallaka na Birtaniya suka kafa iyalan gidan Khalifa ne, wadanda 'yan sunna ne, kuma tun kimanin shekaru hamshin da suka gabata su ne suke mulki a kasar, to amma daga bisani sakamakon tasirin wasu manyan kasashen larabawan yankin tekun fasha a kan wanann masarauta, ta fara nuna banbanci na mazhabar a tsakanin al'ummar kasar, musamman ma a kan mabiya mazhabar shi'a, wadanda su ne akasarin al'ummar kasar.
A cikin yan shekarun baya-bayan nan masarautar bahrain ta tashi ka'in da na'in wajen ganin da murkushe yunkurin da al'ummar kasar suka yi na neman a samar da tsari na dimukradiyya a karkashin tsarin sarautar kasar, inda sarki zai ci gab da mulkinsa, amma a gefe guda a kafa majalisar dokoki wadda 'yan kasa za su zabi mambobinta da kansu, tare da rubuta kundin tsarin mulki, da kuma kafa majalisar ministoci a karkashin Firayi minista wanda majalisa za ta zaba.