IQNA

Jami'an Tasron saudiyya Sun Kame Wani Mai Keta Alfarmar Kur'ani

23:56 - June 17, 2016
Lambar Labari: 3480523
Bangaren kasa da kasa, jami'an tsaron kasar Saudiyya sun kame wani mutum da ake zarginsa da da keta alfarmar kur'ani mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Alriyadh cewa, a jiya , jami'an tsaron kasar Saudiyya sun kame wani mutum da ake zarginsa da da keta alfarmar kur'ani mai tsarki a kasar.

Wannan bayani da jaridar ta kawo ta tabbatar da cewa jami'an tsaron sun kame mutumin wanda dan asalin kasar a yankin Qasim, kuma ya dauki mummuman aikin da ya yi a faifan bidiyo, inda ya watsa a cikin shafin yanar gizo.

Duk kuwa da cewa jami'an tsaron bas u Karin haske kan mutumin ba sunansa da kuma ko shi wane ne da aikinsa , amma dai sun ce dan shekaru talatin da haihuwa ne.

Kasar Saudiyya dai na daga cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya da ake daukar matakai na shiga kafar wando daya da yan kasar masu wulakanta kur'ai kamar yadda yake a rubucea ciki kundin dokar kasar.

captcha