IQNA

Gasar Kur’ani Karo Na Uku A kasar Libya

23:45 - June 18, 2016
Lambar Labari: 3480527
Bangaren kas ada kasa, ana ci gaba da gudanar da gasar kur’ani mai tsarki a garin maslata na kasar Libya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alwsetnews cewa, an fara gudanar da wannan gasa ne tun tun farkon wannan wata na Ramadan mai alfarma a garin Maslata.

Kwamitin da ke kula da ayyukan gasar y bayyan acewa za a ci gaba da gudanar da wannan gasa a dukkanin bangarorinta kmar yadda aka fara gudanar da ita har zuwa raar ashirin da shida.

Mutane 157 ne da suka hada da makaranta da mahardata suke halartar wannan gasa ta kur’ani mai tsdarki, akwai bangaren hardar dukaknin kur’ni, akwai bangaren izihi talatin, sai kuma bangaren izihi sha biyar.

Ana gudanar da wannan gasa takur’ani a masallaci Almujabara da ke garin maslata, kamar yadda aka gudanar a cikin shekaru uku da suka gabata.

  1. 3508023

captcha