
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin jagora cewa, a yammacin Talata ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugabannin bangarori uku na gwamnati (shugaban kasa, shugaban majalisa da alkalin alkalai), manyan jami'an gwamnati, manyan daraktoci na hukumomi da cibiyoyi daban-daban da sauran manyan ‘yan siyasa na kasar Iran inda ya bayyana cewa kara karfafa irin karfi na cikin gida da Iran take da shi a matsayin wata garkuwa ga kasar Iran. Daga nan sai ya ce: Tsari mai kyau da kuma fifita abubuwan da aka fi bukata wasu abubuwa ne da za su taimaka wajen magance manyan matsaloli na koma bayan tattalin arziki da rashin aikin yi da ake fuskanta sannan kuma zai taimaka wajen tabbatar da siyasar tattalin arziki na dogaro da kai.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya fara jawabin nasa ne da kiran mahalarta taron zuwa ga amfanuwa da damar kusaci da Allah da aka samu a watan Ramalana yana mai ishara da wasu addu'oin wannan wata mai alfarma inda ya ce: A wasu daga cikin addu'oin watan Ramalana an bukaci tsira daga zunubai, wanda abin Allah ya kiyaye matukar jami'an gwamnati suka fuskanci wannan matsala, to kuwa cutarwa za ta shafi al'umma da kuma kasa baki daya ne.
Ayatullah Khamenei ya bayyana rashin kuzari, gafala, kaushin zuciya, rashin daukan lamurra da muhimmanci da kuma jiji da kai a matsayin wasu daga cikin irin wadannan zunuban da ake magana, daga nan sai ya ce: Matukar jami'an gwamnati ba su kula da kansu ba sannan suka fuskanci matsalar wadannan zunubai, to a mataki na gaba za su fuskanci wasu zunuban ne da suka fi wannan hatsari da suka hada da munafuncki da karyata ni'imomin Ubangiji.
Don haka Jagoran ya bayyana cewar hanya guda kawai ta tsira daga wadannan zunubai da kauce wa hanya ita ce tsoron Allah da kuma kula da kai.
Daga nan sai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya koma kan batutuwa na yau da kullum inda yayin da yake jaddada cewa a halin yanzu kasar Iran tana cikin wani irin yanayi mai muhimmanci da sarkakiya ne ya bayyana cewar: Daga cikin siffofin da yanayin da ake ciki ya kebanta da su shi ne cewa jami'an gwamnati suna da masaniya sosai kan yanayi da kuma irin karfin da kasar nan take da shi sabanin farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wata siffar ta daban da ta sanya yanayin da ake cikin ya zamanto mai muhimmanci shi ne samuwar wani makiyi na fili da ke kiyayya da Jamhuriyar Musulunci, wanda rikicin da ke tsakani ya wuce rikicin da aka saba tsakanin gwamnatoci.
Haka nan yayin da yake karin bayani dangane da dalilan irin wannan kiyayya ta musamman, Jagoran ya bayyana Jamhuriyar Musulunci a matsayin wani sabon salo maras tamka yana mai cewa: Tsarin Musulunci wanda ya ginu bisa koyarwar irin ta Musulunci yana adawa da girman kai, zalunci, nuna wariya da siyasar tursasawa da amfani da karfi, sannan kuma duk da matsin lambar da yake fuskanta amma a kullum karfi da tasirinsa a yankin nan da kuma duniya sai dada karuwa yake yi da kuma bayyanar da kansa a matsayin wani sabon karfi wanda kuma yake sanya bakaken manufofin kasashe ma'abota girman kan duniya cikin tsaka mai wuya.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wajibi ne a fahimci makirce-makircen makiya sannan kuma mu zamanto muna da wani shiri don fada da hakan.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Dukkanin makirce-makircen makiya shi ne kokarin kawar da irin karfin da Jamhuriyar Musulunci take da shi, idan kuma sun gagara cimma haka, to su dakatar da ci gaban irin wannan karfi da kwarewar da ake da ita.
Haka nan yayin da yake jaddada cewa hanya guda kawai ta fada da wannan makirci na makiya, ita ce ingantaccen amfani sannan kuma wanda ya dace da irin karfi da albarkatun da ake da su da kuma kara karfafa irin karfin da kasa take da shi, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi karin haske dangane da tushen karfin da kasar Iran take da shi.
"Imani da koyarwar Musulunci" shi ne karfi na farko da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da shi inda ya ce: Bangaren da ke tinkararmu yana amfani ne da dukkanin karfin da yake da shi musamman bangaren kafafen watsa labarai na zamani, wajen ganin ya girgiza imani da Musulunci da matasanmu da ma zuriya masu zuwa suke da shi. A saboda haka wajibi ne a ba wa batun karfafa imani da riko da Musulunci da al'umma suke da shi a matsayinsa na daya daga cikin tushen karfi na kasa muhimmanci na musamman.
Ayatullah Khamenei ya bayyana "ci gaban ilimi" a matsayin karfi na biyu da kasar Iran take da shi. Sannan kuma yayin da yake bayanin cewa makiyan al'ummar Iran suna tsananin adawa da ci gaban ilimi da Iran take samu hakan ne ma ya sanya su amfani da makamin kashe masanan Iran, Jagoran ya bayyana cewar: Wadannan mutane a kokarin su na fada da ci gaban ilimin Iran suna amfani hatta da hanyoyin da aka haramta irin su amfani da kuma turo cutar virus ta internet, wanda za mu iya kai kararsu zuwa kotunan kasa da kasa kan hakan, duk da cewa abin bakin ciki ba a yi hakan ba.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Daga daya cikin manyan dalilan matsin lambar da suke yi wa bangaren nukiliya na kasar nan shi ne adawar da suke yi da ci gaban ilimi na kasar na. Don kuwa su kansu sun san cewa da'awar da suke yi na kokarin kera makaman nukiliya, wata karya ce kawai.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana "karfi na tattalin arziki" da "karfi na kare kai" a matsayin wasu dalilai na daban na karfin da kasar Iran take da shi. Sannan kuma yayin da yake jaddada wajibcin kara karfafa irin wannan karfin da ake da shi din, Jagoran ya bayyana cewar: Wajibi ne a kiyaye irin karfi na siyasa na kasa da ake da shi wanda shi ne kiyayye hadin kai da aiki tare duk kuwa da irin sabani na salo na siyasa da ake da shi, wanda babu matsala cikin hakan, to amma wajibi ne a nesanci sabani kan tushen tafiyar wannan tsari na Musulunci.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Cikin yardar Allah a yau din nan akwai hadin kai na kasa dangane da tushen wannan tsari na Musulunci, akasarin mutanen kasar nan suna tare da wannan juyi da alamu da kuma koyarwarsa kamar yadda kuma suke tare da marigayi Imam Khumaini (r.a).
Jagoran ya bayyana "yawan matasa da ake da shi a kasar Iran" a matsayin wani bangare na irin karfin da kasar take da shi inda ya ce: Samuwar matasa wata babbar ni'ima ce kuma mai muhimmanci. A saboda haka wajibi ne jami'an gwamnati su shigo da wani tsari da ya dace wajen kara yawan adadin matasa a kasar nan.
Bayan jaddada wajibci kara irin wadannan tushen karfi da Iran take da shi don fada da makirce-makircen makiya, Ayatullah Khamenei ya jadada cewar: makiya dai su ne "ciyoyin girman kan duniya" karkashin jagorancin gwamnatin Amurka haka nan kuma da "Cibiyoyin sahyoniyawa" wanda alamar su ita ce wannan kagaggiyar gwamnatin sahyoniyawa.
Haka nan kuma yayin da yake cewa makiyan al'ummar Iran ba sa ma boye irin kiyayyar da suke da ita, Jagoran ya bayyana cewar: maganar da ministan harkokin wajen (Iran) yayi a majalisa a 'yan kwanakin da suka gabata na cewa zatin Amurka bai sauya ba, lalle wannan magana ce ta gaskiya. Zatin Amurka a halin yanzu shi ne dai irin wancan zatin Amurka a lokacin mulkin (Ronald) Reagan, sannan kuma babu wani bambanci tsakanin 'yan jam'iyyar Demorats na 'yan Republican.
Ayatullah Khamenei ya yi ishara da wani tunani da ke cike da kuskure da wasu suke yi dangane da Amurkan inda ya ce: Wasu suna tunanin cewa lalle za mu iya tafiya da kuma yin sulhu da Amurka da kuma magance matsalolinmu, alhali kuwa wannan gurgun tunani ne, sannan kuma wani mafarki ne kawai.
Yayin da yake bayyana cewar a hankalce babu wani lokaci da gwamnatin Amurka za ta so Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Mu'amalar Amurka a koda yaushe ta zamanto wata mu'amala ce ta adawa; a saboda haka a yi tunanin cewa matsalar da ke tsakanin Iran da Amurka wani rashin fahimta ne kawai wacce kuma za a iya magance ta ta hanyar tattaunawa ta hanyar riko da salon 50-50, lalle wani tunani ne da ke cike da kura-kurai.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Tushen matsalar Amurka shi ne samuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran wanda ba za a iya magance wannan matsalar ta hanyar tattaunawa da kulla alaka ba. Don kuwa karfi da kuma 'yancin kan da ya samo asali daga tushen Musulunci wani lamari ne da ma'abota girman kai ba za su taba amincewa da shi ba.
Haka nan kuma yayin da yake bayyana cewar a mahangar Amurka, tattaunawa da sulhu yana nufin yin watsi da koyarwar da aka rika ne, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Wannan sassauci da kuma watsi da koyarwar kuwa ba shi da karshe, kamar yadda a halin yanzu bayan cimma yarjejeniya kan nukiliya suka shigo da batun makamai masu linzami, bayan makamai masu linzamin kuma za su shigo da batun hakkokin bil'adama, bayan hakkokin bil'adama kuma za su shiga da batun majalisar kula da kundin tsarin mulki, daga nan kuma sai batu Wilayatul fakih daga karshe kuma sai batun kundin tsarin mulki da kuma gwamnatin Musulunci. A saboda haka tunanin cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta iya cimma sulhu da Amurka, lalle kuskure ne.
Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci ya sake ishara da wani tunani na kuskuren na daban inda ya ce: Wasu suna tunanin cewa dalilin husumar Amurka da Iran shi ne tsokana da kuma kyamar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take nunawa alhali kuwa su din nan su ne tun farkon nasarar juyin juya halin Musulunci suna gina tushen irin wannan kyama da ake musu ta hanyar kulla makirce-makirce, sanya takunkumi, tsokana da kuma ba wa makiyan al'ummar Iran mafaka.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana karfafa "garkuwa da karfin kare kasa" da ake da shi a matsayin magani na hakika na dukkaanin kiyayyar da ma'abota girman kai suke yi wa al'ummar Iran, daga nan sai ya ce: Bisa bayyanannen umurnin Alkur'ani mai girma, wajibi ne mu kara irin karfi na "imani, tattalin arziki, kariya, ilimi, siyasa da yawan jama'a" da muke da shi gwargwadon iyawarmu.
Don haka yayin da yake kiran jami'ai da dukkanin cibiyoyi na gwamnati zuwa ga sauke nauyin da ke wuyansu na kara karfafa karfi da garkuwa ta kasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi jami'an ma'aikatun gwamnati da sauran cibiyoyin da suke da alaka da su zuwa ga la'akari da irin karfi da kwarewa ta ilimi da ake da ita a Iran.
Haka nan yayin da yake jaddada wajibcin goyon baya da kuma karfafa matasa masu riko da koyarwar juyin juya halin Musulunci a matsayinsu na daya daga cikin karfi da kasar Iran take da shi, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Kamar yadda a fili na sha fadi a koda yaushe ina goyon bayan matasa muminai masu riko da koyarwar juyi, sannan kuma lalle ina kaunarsu.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da jawabin nasa ne a yayin wannan ganawar da bayani da kuma jan hankali kan batutuwa guda biyu masu muhimmanci wato bangaren tattalin arziki da kuma yarjejeniyar nukiliya da aka cimma.
Jagoran ya bayyana koma bayan tattalin arziki da rashin aikin yi a matsayin manyan matsalolin kasar Iran, yana mai cewa: Kafin a jingina wadannan matsalolin ga matsalar takunkumi, sun samo asali ne daga siyasa da tsare-tsaren gwamnati mai ci, gwamnatin da ta wuce da kuma wacce ta gabace ta.
Don haka yayin da yake bayanin wasu hanyoyi na magance wadannan matsaloli guda biyu, Ayatullah Khamenei ya bayyana ba da muhimmanci ga kananan sana'oi da na tsaka tsaki a matsayin wani lamari na wajibi, daga nan sai ya ce: Raya irin wadannan sana'oi na daga cikin tushen siyasar tattalin arziki na dogaro da kai. Kuma ya zuwa wani haddi mai girma za su taimaka wajen karfafa tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana tsara ayyuka bisa tushen muhimmancinsu a matsayin lamari mai matukar muhimmanci yana mai cewa: A dabi'ance kowane guda daga cikin ministoci zai ga cewa matsalar da yake fuskanta ita ta fi muhimmanci sannan kuma yana kokari wajen samun albarkatu da yawa. To amma wajibi ne gwamnati ta ba da muhimmanci ga abubuwan da suka fi zama wajibi na hakika wajen karfafa tattalin arziki.
Haka nan kuma yayin da yake bayyana kyakkyawan fatansa dangane da ayyukan da ayyukan tattalin arziki da gwamnati ta ke yi a fagen tattalin arziki na dogaro da kai, Jagoran ya bayyana goyon baya da taimakon kamfanoni masu karfafa harkar ilimi a matsayin lamari mai matukar muhimmanci wajen magance wadannan matsaloli guda biyu na koma bayan tattalin arziki da rashin aikin yi da ake fuskanta.
Ayatullah Khamenei ya bayyana janyo masu zuba jari daga waje a fagagen da ake bukatar hakan a matsayin wani lamari mai matukar muhimmanci, don haka sai ya ce: A wannan fagen ma wajibi ne a lura da bangarorin da suka fi muhimmanci.
Nesantar shigo da kayayyakin da ake da irinsu a cikin gida daga waje ko kuma wadanda ba a bukatarsu a cikin gida, sauya na'urorin da suka lalace a kamfanoni, karfafa bangaren aikin gona da kuma ba da muhimmanci wajen zuba jari a bangaren samar da kayayyakin albarkatun man fetur da sayar da su a waje maimakon dogaro da sai da danyen man fetur suna daga cikin nasihohin da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi wa jami'an gwamnatin.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Kara samar da mai da sayar da shi a waje wata bukata ce da kasar nan take da ita, to amma bai kamata a dinga shigo da man fetur daga waje a kasar da take a matsayin kasar da ta fi ajiyayyun albarkatun man fetur da iskar gas ba. A saboda haka wajibi ne jami'an gwamnati su yi tsare-tsare wajen magance wannan matsalar.
Haka nan kuma yayin da yake sukar masu fadin cewa kasar Iran ba ta da karfin da ke bukata wajen tabbatar da tattalin arziki na dogaro da kai, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Kudaden ajiya na mutane a bankuna suna da wayan gaske; don haka ta hanyar kara irin tallafi da kuma dokokin masu kwadaitarwa za a iya amfani da wadannan albarkatu wajen karfafa siyasar tattalin arziki na dogaro da kai.
Batun yarjejeniyar nukiliya da kuma irin yadda daya bangaren da aka cimma yarjejeniya yake girmama yarjejeniyar shi ne batu na karshe cikin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci mai matukar muhimmanci a yayin ganawarsa da jami'ai da manyan daraktocin gwamnati.
Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar akwai wuce gona da iri cikin mahangar dukkanin bangarori biyu masu goyon baya da kuma masu adawa da yarjejeniyar nukiliyar yana mai cewa: Masu jinjinawa wa yarjejeniyar nukiliyan da kuma masu suka da adawa da yarjejeniyar, a wasu lokuta yayin bayanin mahangarsu suna wuce gona da iri. Alhali kuwa yarjejeniyar nukiliyan tana da bangarori masu kyau kamar yadda kuma take da bangarori na rauni da aibi.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Bangare mai kyau na yarjejeniyar nukiliyan shi ne dai wadannan abubuwan da suka kwadaitar da Jamhuriyar Musulunci zuwa ga zama teburin tattaunawar, duk kuwa da cewa da dama daga cikin wadannan abubuwa masu kyau ba a aiwatar da su ba.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da aibobin yarjejeniyar nukiliyan, Jagoran ya bayyana cewar: wadannan aibobi su ne dai abubuwan da na jima ina ishara da su na cewa daya bangaren dai ba abin yarda ba ne sannan kuma mai karya alkawari ne.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Akwai gibi da nakasi cikin yarjejeniyar nukiliya wadanda idan da an toshe su, to da kuwa an rage irin abin da ake da shi.
Haka nan kuma yayin da yake jinjinawa kokarin da tawagar tattaunar nukiliyan suka yi, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Abin da nake fadi dangane da batun yarjejeniyar nukiliya ba wai ya shafi irin kokari da wahalar da wadannan ‘yan'uwa masu girma suka yi ba ne, face dai ina magane kan ayyukan daya bangaren da aka cimma yarjejeniyar da shi.
Don haka yayin da yake ishara da bangarori masu cike da duhu dangane da yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma wanda shi ne bangaren da daya bangaren yake amfani da shi wajen cimma bakaken manufofinsa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Jamhuriyar Musulunci ta Iran dai ba za ta fara karya yarjejeniyar nukiliyan ba, don kuwa cika alkawari wani umurni ne na Alkur'ani mai girma. To amma matukar aka aiwatar da barazanar da ‘yan takaran shugabancin Amurka suke yi na yaga yarjejeniyar a aikace, to kuwa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta kona yarjejeniyar nukiliyan, wanda hakan ma wani umurni ne na Alkur'ani dangane da karya alkawarin da daya bangaren yayi.
A ci gaba da jawabin nasa Ayatullah Khamenei yayi karin haske dangane da rashin cika alkawarin Amurka da kuma rashin aiki da nauyin da ke wuyanta inda ya ce: Nauyin da ke wuyan daya bangaren shi ne dage takunkumin, to amma ba ta yi aiki da hakan ba. Wato ta wani bangaren an dauke wasu takunkumin, to amma a aikace ba a dauke takunkumin ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Amurkawa sun ci gaba da kiyaye asalin takunkumin, wanda hakan yana da tasiri cikin kananan takunkumin da aka dage din.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wajibi ne jami'an da abin ya shafa su yi la'akari da hakan, kada su dinga fadin cewa an dage takunkumi.
Haka nan yayin da yake ishara da rashin dage mu'amala da bankunan kasashen waje, Jagoran ya ce: Jami'an Amurka a baki da kuma kan takarda suna fadin cewa babu wani abin da zai hana mu'amala da bankunan Iran, to amma a aikace suna yin abubuwan da suke sanya tsoro cikin mu'amala da Iran.
Ayatullah Khamenei ya bayyana maganar daya daga cikin jami'an Amurka na cewa "ba za mu taba barin Iran ta zauna lafiya ba" a matsayin misali na irin wannan mu'amala mai harshen damo ta Amurkan. Daga nan sai ya ce: Wannan shi ne irin abubuwan da Amurkawa suke yi wajen yin kafar ungulu ga mu'amalar bankunan Iran da na kasashen waje, a saboda haka bai kamata wani ya dinga neman halalta wannan aiki na Amurka ba.
Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da kudaden kasar Iran da aka kwace a kasashen waje yana mai cewa: A halin yanzu shigo da kudaden man fetur da aka sayar ma wani lamari ne mai wahalar gaske, sannan kuma har ya zuwa yanzu muna da kudade a wasu bankunan wasu kasashen wadanda ba a dawo da sub a. Hakan kuwa saboda wadannan kudaden a dalar (Amurka) suke, sannan kuma an kulle su sakamakon kiyayya da kuma rashin cika alkawarin Amurka.
A ci gaba da jawabin nasa Ayatullah Khamenei ya bayyana fasahar nukiliya a matsayin wani lamari mai matukar muhimmanci gaske wanda wajibi ne a ci gaba da karfafa da kuma fadada ta.
Jagoran ya kirayi jami'an gwamnatin da su kiyaye irin ci gaban da Iran ta samu a wannan bangaren da kuma tsayawa kyam wajen fada da duk wani kokarin kafar ungulun Amurka a wannan bangaren yana mai cewa: Hakki dai wani abu ne da ake kwato shi shi din ma a bakin bakar kura irin Amurka, wanda wajibi ne a kwato hakki daga bakinta.
Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musuluncin, sai da shugaban kasar Iran Hujjatul Islam wal muslimin Dakta Hasan Ruhani ya gabatar da jawabinsa dangane da irin ayyuka da nasarorin da gwamnatinsa ta samu da kuma irin ayyukan da za ta sa gaba a nan gaba.