
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar Alalam cewa, a yau kotun masarautar Bahrain ta sanar da cewa an janye shedar zama dan kasa daga kan sheikh Isa Kasim babban malamin addini a kasar.
Wannan bayani daio ya zo yan kwanaki bayan fara daukar wasu matakai na takura ma mabiya mazhabar shi’a wadanda su ne masu rinjaye a kasar, sakamakon hakurin da suke yin a tsawon shekaru ba tare da mayar da wani martini kan irin zaluncin da suke fuskanta ba.
Tuna makon da ya gabata masarautar Bahrain ta kirayi wasu daga cikin manyan malaman addini domin yi musu tambayoyi a kan wasu batutuwa da ba a bayyana ba, amma malaman sun yi kira da a dakatar da sallolin juma da na farilla domin nuna rashin amincewa da matakan takura musu.
Sheikh Majid Almash’al shugaban mjalisar malaman addini a kasar mljalisar malaman mabiya mazhbar shi’a wadda it ace majalisa ta malamai mafi girma a kasar, yana daga cikin wadanda aka kira domin jamusu kunai kan su daina taba sarki a kan duk wata tabargaza da ya tafka.
Wannan mataki dai ya fusata al’ummar kasar, inda a yau baki dayan kasar ana ci gaba da nuna rashin amincewa da hakan, tare da yin kira ga masarautar ta mulkin mulukiya da ta gaggauta janye wannan hukunci ba tare da bata lokaci ba, ko kuma kasar ta shiga wani yanayi wanda sai abin da hali ya yi.