
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alfajr cewa, wannan matashimai suna Nabil Ahmad ya fara gudanar da wannan aiki da nufin bunkasa harkokin da suka shafi kur’ani mai tsarki a kasarsa wanda zi kasance a cikin 120x160cm.
Nabil Ahmad ya ce ya fara gudanar da wannan aiki ne tun daga ranar frko ta watan Ramadan mai alfarma, inda a cewarsa acikin kwanaki 10 na farkon wannan wata mai albarka an kamala shafuka na farko na wannan rubutun kur’ani.
Ya ci gaba da cewa ya zuwa an mayar da wannan shiri na rubuta kur’ani mafi girma da rubutun hannu zuwa dandalin salahuddin Alayyubi, domin bayar da dama ga mutane da suke da bukata su shiga cikin shirin.
Wannan shiri na rubuta wannan kwafin kur’ani wanda shi ne irinsa na farko a kasar ta Masar, zai ci gaba da nan har zuwa watan azumi na shekara mai zwa, inda ake sa ran za a kamala shirin da yardarm ubangiji.
Tun a cikin shekara ta 2011 aka shirya gudanar da wannan shiri na rubuta kur’ani mafi girma da rubutun hannu a kasar Masar a lokacin Farouq Hasani yana ministan yada al’adu, amma saboda hatsaniyar da ta kaule a cikin kasashen larabawa, wannan shiri bai yuwu ba sai yanzu da aka dan samu kwanciyar hankali a kasar.