
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga bangaren yada labarai na cibiyar yada al’adun muslunci ta jamhuriyar muslunci cewa, an gudanar da gasar a tsakanin dalibai kimanin 90 daga makarantun Imam Mahdi (AJ) Adabin mulsunci, ilimin muslunci da kuma Ibrahimiyyah.
Ita dai wannan gasa an shirya ta ne da nufin tunawa da lokacin zagayowar haihuwar Imam Hassan Almujaba (AS) wanda karamin ofishin jakadancin jamhuriyar muslunci ya daui nauyin shiryawa a kasar.
An samu halartar mayan malaai da kuma alkalan gasar kur’ani wadanda suke da gogewa ta yin alakalnacin gasar kur’ani ta kasa da kasa, wanda hakan ya baiwa gasar wani launi na musamman.
Gasar dai an kasa zuwa kasha daban-daba, inda wasu suke gudanar da itaabngaren hardar kur’ani baki daya, wasu rabinsa, yayin da kuma daga rub’insa a bin da ya yi kasa, an kuma bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo a wannan gasa.
Awam Sulaiman daga makarantar Adabin muslunci ita ce ta zo ta daya a bangaren kira’a, sai kuma Muhammad Abduljalil wanda ya zo na biyu daga makarantar koyon ikimin mulsunci, Habibatu Habib mataki na uku daga makarantar Imam Mahdi (AJ), sai kuma Ibrahim Abubakar na mataki na farko daga makarantar adabin muslunci, Mukhtar Tajuddin mataki na biyu, sai kuma Muhammad Mukhtar daga makarantar Ibrahimiyya mataki na uku.