Gasar dai ta samu halartar matasa makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki
daga wasu daga cikin kasashen yammacin Afirka da suka hada da ita kanta kasar
ta Senegal da Mauritaniya, Mali, Gambia da sauransu, kamar yadda kuma wasu daga
cikin manyan malaman addini musamman na darikar Tijjaniya da wasu darikokin
sufaye na kasar da kuma wasu 'yan siyasa sun halarci wurin.
Shugaban ofishin yada al'adun muslunci na kasar Iran a Senegal Sayyid Hassan
Ismati ya gabatar da jawabi a wurin, inda ya bayyana cewa kur'ani mai tsarki da
sunnar manzon Allah su ne za su hada musulmi baki daya a wuri guda duk kuwa da
irin banbancin fahimta kan wasu mas'aloli da ke tsakaninsu, amma wadannan
manyan abubuwa biyu kur'ani da sunnar ma'aiki sun hada su.
Daga cikin wadanda agayyata domin yin alkalanci a wurin wannan gasa, akwai baki
daga kasashen Libya, Kuwait, Saudiyyah, Iran, da kuma Masar, a karshen taron an
bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo a bangarorin gasar.