IQNA

Hojjatol Islam Siddighi:

Al Saud Da Al Khalifa Za Su Tsere Kamar Yadda Shah Ya Tsere

23:42 - June 24, 2016
Lambar Labari: 3480544
Bangaren siyasa, wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran yayi Allawadai da janye hakkin zama dan kasa daga kan sheikh Isa Kasim da mahukuntan Bahrain suka yi, tare da bayyana cewa lokaci ne wata rana za a neme su a rasa kamar yadda aka ne sarki shah aka rasa.

Kamfanin dillanicn labaran kur’ani na Iqna ya habarta cewa, Limamin da ya jagoranci salar Juma'a a nan birnin Tehran ya ce mumunar mu'amalar da masarautar Ali Khalifa ke yiwa Al'ummar Bahren ya sabawa Adamtaka kuma ta tare da mumunan sakamako.

A yayin da yake bayyana damuwuwarsa kan mumunar mu'amalar da masarautar Ali Khalifa ke yi kan Al'ummar Baharen wajen hana su gudanar da jerin gwano, Limamin da ya jagoranci salar Juma'a a nan birnin Tehran Hujjatu-islam Kazim Siddiki ya ce babu abinda Al'ummar Bahren din ke bukata face hakkokinsu ta hanyar lumana da zaman lafiya.

A cikin shekaru biyar da suka gabata Al'ummar Bahren din sun fuskanci takura da cin zarafi daga magabatan kasar inda da zarar sun fito zanga-zangar Lumana ake mayar musu da martani da harshashe, kuma hakan na zuwa ne bisa umarnin masarautar Ali sa'oud.

Daure maluma a gidan kaso da kuma karbe takardar dan kasa a kasashen Bahren da Saudiya zalunci ne, kuma shakka babu magabatan masarautar Ali khalifa da Ali sa'oud su jira mumunan sakamako a kan wannan zalinci na su.

A yayin da ya koma kan fatawar da maliman Yahudu suka bayar na halacin batan ruwan sha na Al'ummar Palastinu, Hujjatu Islam Kazimi ya ce wannan Fatawa ta yi hanun riga da karantaswar Annabi Musa (a.s).

Yayin ya koma kan cire sunan Saudiya a jerin kasashen da ke take hakin kananen yara saboda yadda suka yiwa Yaran kasar Yemen kisan killa, HUjjatu-islam Siddiki ya tabbatar da cewa wannan mataki da MDD ta dauka ya zamanto wani babban kuskure da babu yadda za ta yi ta gyara shi a nan gaba kuma hakan shi ke nuna cewa Majalisar na kalkashin tasiri karfi da kuma batun dukiya ne kawai ,domin haka babu yadda za a yi Al'ummar Duniya su yi jiran irin wannan Majalisa za ta kare mata hakkokinsu.

Har ila Yau Limamin ya ce shurun da MDD ta yi a kan kananen yara, miskinai , wadanda suka samu rauni, marayu da kuban milyoyin mutane dake fuskantar barazanar Yunwa a kasar Yemen, laifi ne da babu yadda za a yi a karbi uzurinsa, kuma hakan ya dora Ayar tambaya ga halarcin Majalisa.

3509972

captcha