IQNA

Kafofin Yada labaran UAE: Wani Dan Turai Zai Lashe Gasar Dubai

23:44 - June 24, 2016
Lambar Labari: 3480545
Bangaren kasa da kasa, kafofin yada labaran hadaddiyar daular larabawa suna bayar da rahoton cewakwai yiwuwar a karon farko wani daga nahiyar turai zai lashe gasar kur’ani ta Dubai.

Kamfnin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na abra Emarat cewa, gasar kur’ani ta duniya da aka gudanar a birnin Dubai ta kawo karshe.

Baynain y ace a karon farko ana sa ran wani mahardacinkur’ani daga nahiyar turai zai lashe wannan gasa a mataki na farko wanda kuma wakilin Holland ne.

Wannan makaranci kuma mahardaci sunan Balal Imani, kuma ya bayar da mamaki matuka gas u aknsu alkalan gasar, yadda ya rika amsa dukkanin tambayoyin da suka yi masa.

Duk da cewa a ranar karshe yay i jure daya, amma tun daga nan har aka kamala bai sake yin wani kure da aka yi masa gyara ba.

Wannan gasa dai an kamala ta ne tun a ranar Laraba da ta gabata, amma ana jirn kamala dukkanin nazari daga alkalan gasar, inda daga karshe za a sanar da sunayen wadanda suka lashe gasar mataki-mataki.

Gasar wadda ake gudanarwa a karo an ashirin tana samun halartar wakilai daga kasashe 82 na duniya, kuma ta hada bangarori na harda da kuma kira da ka’idojin sanin hukncin karatu gami tfsiri da sauransu.

Ali Reza Lu dais hi ne yake wakiltar jamhriyar muslunci ta Iran a wannan gasa, kma ya je har zuwa mataki na karshe.

3509959

captcha