IQNA

Shirin Iran Na Koyar Da Daliban Jami’a Ilmomin Kur’ani A Uganda

23:34 - June 26, 2016
Lambar Labari: 3480554
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da wani shiri na koyar da karatun kur’ani mai tsarki ga daliban jami’ar birnin Kampala.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al’adu ta jamhuriyar muslunci cewa, an fara gudanar da wani shiri na koyar da karatun kur’ani mai tsarki ga daliban jami’a na kasar Uganda a masallacin jami’ar Kampala fadar mulkin kasar.

Shirin dai ya fara da mutane 20 ne, inda ake koyar da su karatu da kuma sanin ma’anonin ayoyin kur’ani mai tsarki da wasu ilmomi da suka shafi kur’ani.

Ofishin yada al’adun mulsunci na jamhuriyar muslunci ta Iran ne dai ya dauki nauyin wannan shiri, bayan da kungiyar daliban jami’a musulmi ska gabatar da wannan buka ga ofishin.

Jami’ar Kampala dai it ace jami’a mafi girma a kasar Uganda, kuma dalibai musulmi suna gudanar da harkokinsu na addini a cikin yanci.

3510475

captcha