Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga
shafin sadarwa na yanar gizo na kamafanin dillancin labaran kasar Faransa cewa,
Wasu 'Yan kunar Bakin wake da ake
kautata zaton 'yan Boko haram ne sun kai hari a wani Masallaci na garin
Maiduguri.
A Najeriya, wasu 'yan kunar-bakin-wake da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun rasa ransu bayan da bama-bamai suka tashi da su a lokacin da suke kokarin shiga wani masallaci daren jiya lahadi a birnin Maiduguri da ke jihar Borno.
Rahotanni na cewa maharan dai sun je masallacin ne da nufin shiga sahun Sallah a lokacin da jama'a suke tsaka da Sallar dare da aka fi sani da Kiyamullaili, a wani masallaci da ke Damboa Road.
Wani ganau ya shaida wa manema labarai cewa 'yan kunar-bakin-waken ne kawai suka hallaka.
Yanzu haka dai an tsaurara matakan tsaro a kusan dukkanin masallatan da ke birnin na Maiduguri.
A bangare guda, Majiyar tsaron Sojin kasar ta sanar da ceto Mazauna kauyukan arewa maso gabashin kasar 6 da adadinsu ya kai dubu biyar tare kuma da tsarkake su daga mayakan boko haram.