IQNA

21:55 - June 27, 2016
Lambar Labari: 3480559

Mabiya Addinin Buda Na Keta Alfarmar Masallatan Musulmi A Myanmar

Bangaren kasa da kasa, Masu tsattsauran ra'ayi na mabiya addinin Buda a kasar Myanmar suna ci gaba da cin zarafin musulmi da keta alfamar masallatai da wuraren ibada na mabiya addinin muslunci.

Mabiya Addinin Buda Na Keta Alfarmar Masallatan Musulmi A Myanmar
Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na Iqna ya habarta cewa, Tashar talabijin ta alalam ta bayar da rahoton cewa, a cikin 'yan kwanakin nan 'yan buda masu tsattsauran ra'ayi sun ci zarafin musulmi a wurare da dama a cikin kasar Myanmar, kuma hakan yana faruwa ne tare da cikakken goyon bayan gwamnatin kasar, tare da yin rufa-rufa wajen hada labarin hakan ya watsu a duniya.

Rahoton ya ce baya ga hain da 'yan buda suka kai a daren Juma'ar da ta gabata a garin Bago, inda suka rusa babban masallacin musulmi tare da banka masa wuta, sun kai hare-hare a wasu sassa na kasar a kan musulmi, inda suka keta kwafi-kwafi na kur'ani mai tsarki, amma kafofin yada labaran kasar suna boye labarin.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa wadanda suka hada har da Amnesty Int. a cikin wannan makon sun bukaci da a gudanar da binciken gaggawa kan abin da yake faruwa na cin zarafin musulmi a kasar Myanmar, tare da daukar matakai na kare rayukansu da dukiyoyinsu, da kuma gurfanar da duk wanda aka samu da hannun wajen muzgunawa musulmi a gaban kuliya.

3510704

captcha