
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-sharq cewa, wannan cibiya mai suna RAF karkashin jagoran Sheikh Thani bin Abdullah da ke gudanar da ayyukan agaji, ta bude rassanta nea yankin Ajara, inda za a koyar mutane dubu20 karatu da hardar kur’ani mai tsarki.
Dukkanin rasan cibiyar da aka gina suna ajujuwa 3 da kuma masalalci gami da wurin alwalla, sa kuma dakin karatu, gami da wuraren zama domin koyon hardar kur’ani mai tsarki.
Darussan kur’ani da za a rika koyar da yara za su kasance ne karkashin jagoranci malamai kwararru wadanda za su iya tarbiyantar da yara akan karatu da hardar kur’ani.
Wannan cibiya ta Alrahama dai tana gudanar da ayyukanta na jin a cikin kasashe daban-daban na duniya musamman wadanda suke da bukatar taimako wannan fuska.
Abin tuni a na dai shi ne, kasar Kenya, tana da mabiya addinin muslunci kimanin miliyan 10 da suke rayuwa a cikinta, wato kimani kasha 30 cikin dari na mutanen kasar kenana, kamar yadda kuma muuslmi dubu 300 ne suke rayu a cikin birnin Nairobi, wanda shi ne fadar mulkin kasar.