
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Indepent cewa, cibiyar Tell Mama ta bayar da rahoton cewa a cikin shekarar da ta gabata kyamar musulmi ta karu da kasha 326 cikin dari a kasar, kuma yanzu lamarin yana karuwa.
Rahoton ya ce mata mabiya addinin muslunci suna fuskantar matsaloli a cikin rayuwarsu ta yau da kullum saboda da saka hijabi da suke yi.
Haka nan kuma rahoton ya yi nuni da cewa kimanin kasha 61 na mutanen da suka fi fuskantar wannan matsala mata, saboda an fi saurin gane su saboda tufafinsu.
Rahoton cibiyar Tell Mama ya kara da cewa, wadanda suka fi shiga cikin kungiyoyin masu kyamar musulmi a kasar dai matasa ne, wadanda shekarunsu bas u wuce 13 zuwa 18 ba.
Shahed Malek shi ne shugaban cibiyar ta Tel Mama kuma tsohon minister ne na ayyuka a kasar ta Birtaniya ya bayyana cewa, yanayin da ake ciki na kyamar musulmi a kasar ba abu ne mai kyau ba.
Shoja Shafi shi ne babban sakataren majalisar musulmin Birtaniya ya bayyana cewa, a halin yanzuana cikin wani mawuyacin halia cikin kasar ta fuskar siyasa da zamantakewa.