IQNA

An Fara Gudanar da Hardar Kur'ani mai Tsarki A Garin Gado Na Libya

23:54 - June 29, 2016
Lambar Labari: 3480563
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki ta garin gado an kasar Libya a jiya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Akhbar Libya cewa, a jiya an fara gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki ta garin gado an kasar Libya da ke arewacin kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa tana daya daga cikin irinta da ake gudanarwa a kowace a cikin watan Ramadan wadda ta hada makaranta da mahardata daga sassa na gundumar.

An dauki loaci ba a gudanar da wannan gas aba saboda yanayin da kasar take ciki na rashin tabbas ta fuskar tsaro, amma a halin yanzu an samu dan daidaton lamurra fiye da baya.

Kimanin mahardata 81 ne daga cibiyoyin kur'ani guda 10 suke halartar wannan gasa, inda suke karawa da juna, daga karshe kuma za a bayar da kayutuka ga wadanda suka nuna kwazo.

Babbar cibiyar kula da harkokin kur'ani ta yankin ce dai ta dauki nauyin shirya gasara wannan karo, kuma ta samu karbuwa daga yankunan kasar da ke makwabtaka da yankin, wand ake fatan daga wannan shekara za aci gaba da gudanar da ita kamar yadda aka saba.

3511130

captcha