IQNA

Ganawar Jagora Da Bangaren Shari’a:

Wajabcin Kare Hakkonin Palastinawa Ta Hanyar Daga Murya A Ranar Quds

23:44 - June 30, 2016
Lambar Labari: 3480566
Bangaren siyasa, Ayatolah Khamenei a lokacin da yake ganawa da manyan jami’ai na bangaren shari’a a jamhuriyar muslunci ya byayana wajabcin hada karfi da karfe domin kare hakkokin al’ummar Palastinu ta hanyar daga murya da isar da wannan sako a ranar Quds ta duniya.

Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin jagora na yanar gizo cewa, a yammacin yau Laraba ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da alkalin alkalai da sauran manyan jami'an bangaren shari'a na gwamnatin Iran, inda a jawabin da ya gabatar ya bayyana ingancin ma'aikatar shari'a da kuma kokari wajen samun yarda da amincewar mutane a matsayin wani nauyi mai muhimmanci kana kuma babbar manufar ma'aikatar shari'ar. Haka nan kuma yayin da yake ishara da kusatowar Ranar Qudus ta Duniya ya bayyana cewar: Da yardar Allah a ranar Juma'a mai zuwa din nan al'ummar Iran da sauran al'ummomin duniyar musulmi za su fito don nuna goyon bayansu ga al'ummar Palastinu da ake zalunta, sannan kuma al'ummar musulmi za ta sauke nauyi mai muhimmanci da ke wuyanta na kare wadanda ake zalunta.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya fara jawabin nasa ne da ambato da kuma jinjinawa tsohon alkalin alkalan Iran Ayatullah Shahid Beheshti wanda ya bayyana shi a matsayin kwararren shugaba mai gaskiya da rikon amna, kamar yadda kuma ya gode da kuma jinjinawa jami'an ma'aikatar shari'a saboda irin kokari da aiki tukurun da suke yi.

Haka nan kuma yayin da yake jinjina wa shugaban ma'aikatar shari'ar kuma alkalin alkalan na Iran a matsayin malami masani, Jagoran ya bayyana cewar: Ma'aikatar shari'a tana da tasirin gaske a fagen sanya ido wajen ganin an aiwatar da doka da kuma fada da laifuffuka, haka nan kuma kasantuwar alkalin alkalan cikin majalisar koli ta kasa hakan lamari ne mai tasirin gaske cikin manyan siyasosi na kasa.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Bisa la'akari da wannan muhimmanci ne ya sanya a koda yaushe matsaya da ayyukan ma'aikatar shari'a suke da muhimmanci na musamman, hakan ne kuma ya sanya a koda yaushe (masu bakar aniya) suke tsanantawa wajen kokarin shafa mata bakin fenti.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A halin yanzu irin bakar farfagandar da kafafen watsa labaran ‘yan kasashen waje suke yadawa kan ma'aikatar shari'a ta karu sosai, hakan kuwa ya samo asali ne sakamakon matsayar da shugaban ma'aikatar shari'ar da kuma manyan jami'anta suke dauka ne wadanda suka yi daidai da koyarwar juyin juya halin Musulunci.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da batun janyo hankulan mutane da kuma neman yardarsu a matsayin wani nauyi na Musulunci kana kuma babbar manufa, Jagoran ya bayyana kiyaye ingancin ma'aikatar shari'ar a matsayin babban abin da zai janyo hankula da kuma yardar mutane ga ayyukan ma'aikatar shari'ar. Daga nan sai ya ce: Wajibi ne a yi fada da kuma nuna halin ba sani ba sabo da baragurbin da suke cikin ma'aikatar shari'ar. Wajibi ne a ci gaba da hakan.

Jagoran ya kirayi jami'an ma'aikatar shari'ar da cewa: Ku sanya batun tabbatar da inganci da gaskiyar ma'aikatar shari'ar a matsayin babban aikin da ke gabanku da kuma daukar hakan a matsayin tushen aikinku.

Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada wajibcin sanar da mutane irin matakan da aka dauka wajen fada da masu laifi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: ‘Yan wasu tsirarrun da suke cikin ma'aikatar da suke aikata laifi da abubuwan da suka saba wa doka, baya ga ha'intar shugabanni da daraktocin ma'aikatar da suke gudanar da aikinsu tukuru, har ila yau kuma suna zaluntar sauran ‘yan kasa ne.

Ayatullah Khamenei ya kirayi jami'an ma'aikatar shari'ar da su ba da muhimmnaci ga tsare-tsaren da suka dace wajen fada da laifuffuka, kamar yadda kuma ya kiraye su da su yi iyakacin kokarinsu wajen rage zartar da hukuncin dauri a gidan yari inda ya ce: Wajibi ne a yi aiki da masana da kwararru wajen samo hanyoyin da za a maye gurbin hukuncin dauri a gidan yari da wani hukuncin na daban.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana sanar da mutane irin ayyukan da ma'aikatar shari'ar take yi a matsayin daya daga cikin ayyuka masu muhimmnacin gaske yana mai cewa: Wajibi ne a bisa hanyoyin da suka dace wajen sanar da jama'a irin gagarumin aikin da ma'aikatar shari'ar take yi.

Har ila yau Jagoran ya kirayi jami'an ma'aikatar shari'ar da su ba da himma wajen koyar da jama'a batutuwan da suka shafi shari'ar da kuma hakkoki wanda ya ce hakan zai rage irin yadda jama'a yawan kai kara kotuna, kamar yadda kuma ya bayyana bin lamurran da suka shafi hakkoki na kasa da kasa a matsayin wani lamari da ya zama wajibi ma'aikatar shari'ar ta ba shi muhimmanci inda ya ce: Wajibi ne a ma'aikatar shari'a ta sanya bin diddigin hakkokin al'ummar Iran da aka take sakamakon takunkumin da aka sa a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan da ke gabanta.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da hukuncin da wata kotun Amurka ta yanke na rike dukiyoyin al'ummar Iran da suke kasar bisa wasu tuhumce-tuhumce marasa tushe, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Tauye hakkokin al'ummar Iran sakamakon takunkumin da aka sanya musu, wani lamari da yake a fili wanda wajibi ne a bi diddigin lamarin a fage na kasa da kasa.

Bin diddigin dubban al'ummar Iran da suka cutu sakamakon ayyukan ta'addancin da aka yi musu a Iran, kai karar gwamnatocin da suka ba wa wadanda suka kai wadannan hare-hare na ta'addanci mafaka da kuma goyon bayansu a fili da kuma kare hakkokin musulmi da aka zalunta a duk fadin duniya, suna daga cikin batutuwan da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada muhimmancinsu ga jami'an ma'aikatar shari'ar.

Ayatullah Khamenei ya bayyana bayyanar da mahangar Musulunci dangane da hakkokin bil'adama a tsakanin al'ummomin duniya a matsayin wani nauyin da ke wuyan ma'aikatar shari'ar inda ya ce: An gina hakkokin bil'adama na kasashen yammaci ne bisa tushe na kuskure, a saboda haka wajibi ne a yi wa duniya bayanin tushen hakkokin bil'adama na Musulunci wanda ya ginu bisa ingantattu da karfafan tushe.

Jagoran ya bayyana irin rufe idon da Majalisar Dinkin Duniya ta yi dangane da take hakkokin kananan yaran kasar Yemen da cire sunan Saudiyya daga cikin masu take hakkokin kananan yaran da ta yi saboda kudi a matsayin wani abin kunya. Daga nan sai ya ce: Wannan abin kunyan shi ne hakikanin take hakkokin bil'adama.

Kafin jawabin Jagoran sai da Ayatullah Sadiq Amoli Larijani, alkalin alkalai kuma shugaban ma'aikatar shari'ar ta Iran ya gabatar da jawabinsa inda yayi karin haske kan irin ayyukan da hukumar ta sa ta aikata da kuma abubuwan da ta sa a gaba.

3511538

captcha