IQNA

Harin Kunar Bakin Wake A Kusa Da Masallaci A Kamaru / Mutane 11 Sun Mutu

23:47 - June 30, 2016
Lambar Labari: 3480567
Bangaren kasa da kasa, Mutane ashirin da takwas aka tabbatar da sun kwanta dama a tagwayen hare hare a kasar Kamaru.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na Press TV cewa, Mutane ashirin da takwas ne jami'an tsaro a arewacin kasar Kamaru suka tabbatar da mutuwarsu .

An nakalto majiyar sojojin kasar ta Kamaru tana fadar haka a jiya laraba, ta kuma kara da cewa hare haren bom ne guda biyu wadanda aka kai a cikin garin Djamkana daga arewacin kasar.

Sai dai majiyar bata bayyana wadanda suka kai hare haren ba kuma ba wanda ya daunauyin hakan. Amma shugaban kasar ta Kamaru Poul Biya ya tabbatara da aukuwar harin ya kuma bayyana cewa wannan aikin kungiyar yan ta'adda ta bokoharam ce.

Tun cikin shekara ta dubu biyu da uku ne mayakan boko haram suka kaddamar da hare haren a cikin kasar Kamaru wanda ya kai ga rasa rayukan mutane da dama da kuma jikkata wasu. Majiyar tsarokasar Kamaru ta bayyana cewa tun watan Janairuna wannan shekara ya zuwa yanzu kimani mutane dari ne suka rasa rayukansu sanadiyyar hare haren boko haram.

3511615

captcha