
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, Hojjatol Islam Sayyid Ahmad Khatami wanda ya ke gabatar da huduba a yau juma'ar karshe ta watan Ramadhan wacce ita ce ranar qudus ta duniya, ya kara da cewa; Musulmi al'umma guda daya ce wacce ta ke karkashin inuwa guda, saboda haka ba za su taba samun nutsuwa ba matukar ba a 'yanto da palasdinu ba daga mamayar 'yan sahayoniya ba.
Gabanin Sallar juma'a a Tehran din miliyoyin al'ummar Iran sun gudanar da zanga-zanga a fadin kasar domin raya ranar qudus.
A cikin kasashe da dama na duniya an yi irin wannan zanga-zangar da su ka hada da Lebanon da kuma Yamen.
A yau ne dai ranar Juma'ar karshe ta watan Ramadan al'ummomi daban-daban na duniya ke gudanar da tarukan ranar Quds, domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu da ke karkashin zaluncin yahudawan Isra'ila, da kuma jaddada alkawali na kare wurare masu tsarki da ke palastinu, wanda masallacin Quds ke kan gaba.
Gwamnatin kasar Iran ta sanar da cewa, za a fara gudanar da jerin gwano na ranar Quds ta duniya a garuruwa 850 na a kasar daga karfe goma da rabi na safiyar yau, inda dukkanin al'umma gami da malamai na sunna da shi'a na kasar baki daya za su fito a cikin sahu guda, domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu, da kuma jaddada wajabcin 'yantar da masallacin Quds mai alfarma daga mamamyar yahudawa.
Marigayi Imam Khomeni wanda ya assasa Jamhuriyar muslunci ta Iran ne dai ya ayyana wannan rana ta Juma'ar karshen kowane watan ramadan ta zama ranar Quds ta duniya, domin raya ruhin al'ummar musulmi dangane da mamayar da yahudawan sahyuniya suke yi a kan wannan masallaci mai tsarki, alkiblar manzon Allah (SAW) ta farko, da kuma nuna goyon baya ga Palastinawa da ke karkashin zaluncin yahudawa.
A tarayyar najeriya ma an gudanar da Zanga-zangar ta lumana a cikin biranen katsina da Potuskum, yayin da ake shirin gudanar da iya idan an idar da sallar juma'a a birnin kano.
Masu Zanga-zangar a birnin katsina sun daga kwalye da kyallaye dauke da taken yin tir da zaluntar al'ummar Palasdinu da 'yan sahayoniya su ke yi.
A garin Potuskum da ke Jahar Yobe ma an sami dandazon masu zanga-zangar da su ka fito daga cikin birnin da kuma garuruwan da su ke kusa.
A kowace shekara dai harkar musulunci a karkashin Sheik Ibrahim Yakub al-zakzaky tana gudanar da zanga-zangar ranar qudus ta duniya daidai a ranar juma'ar karshe ta watan Ramadhan bisa amsa kiran jagoran juyin musulmi, Marigayi Imam Khumain (RA) da ya assasa wannan lamari.