Kamfanin
dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar
gizo na alakhbar.ifo cewa, a jiya ne aka kamala gasar kur’ani ta kasar
Mauritaniya tare da bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo, wato Akah
Wuld Abyatat daga Mauritaniya na daya, Hisham Dawi daga Algeriya na biyu, sai
kuma Mudi Jub daga Gambia na uku.
Bayanin ya ce wanda ya zo a mataki na daya ya samu miliyan 3 na Augya wato kudin Mauritaniya wanda yake duk augya dari biyu ne ke yin yuro daya, an bayar da augya miliyan daya da rabi ga dukkanin wakilan Algeriya da Gambia da suka suka zo a matsayi na biyu da na ukua gasar.
Tun kimanin kwanaki uku da suka gabata ne aka fara gudanar da gasar kur’ani ta Mauritaniya, tare da halartar wakilai daga kasashen, Tunisia, Algeriya, Morocco, Mali, Gambia da kuma Senegal, mai taken gasar shugaba Muhammad Wuld Abdulaziz shugaban kasar ta Muritaniya.