Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin malaman jami'oi a kasar Masar sun bakaci babbar cibiyar addini ta kasar Azhar, da ta cire wasu daga cikin ayoyin jihadi daga manhajarta ta koyarwa, domin kauce wa yin amfani da hakan wajen ayyukan ta'addanci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin
sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi wadda ta buga a shafinta na yanar gizo
a yau cewa, wasu fitattun malaman jami'a na kasar sun bukaci Azahar da ta cire
ayoyin da ke yin kira zuwa ga jihadi ne, domin 'yan ta'adda suna daukar
wadannan ayoyin ne kawai daga cikin kur'ani domin baka kansu hujja wajen aikata
ta'addanci da sunan jihadi, suka a maimakon haka a mayar da hakankali a kan
ayoyin da suke kira zuwa ga zaman lafiya da rahama da tausayia tsakanin 'yan
adam.
Shi ma a nasa bangaren ministan harkokin al'adu na kasar ta Masar Jabir Asfur
ya nuna goyon bayansa ga wannan kira na malaman jami'oin kasar ta Masar ga
cibiyar Azahar, inda a cewarsa hakan baya yana nufin rashin amincewa da ayoytin
ba ne, illa dai yin amfani da hikima wajen kauce wa duk wani aiki na bata sunan
muslunci tare da fakewa da ayoyin kur'ani.
Tun kafin wanann lokacin dai gwamnatin kasar Morocco ta sanar da cire ayoyin da
suke yin kira zuwa ga jihadia cikin manhajar koyarwa amakarantun kasar, da suna
kauce wa yin amfani da hakan wajen aikata ta'addanci da sunan jihadi.
3512319