Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin yanar
gizo na jaridar Independent ta kasar Birtaniya wadda ta bayar da rahoton cewa,
musulmi sun dauki wannan mataki na rashin gudanar da sallar idin karamar a
salla a bana ne saboda karuwar kymar baki musamman ma musulmi a a birnin.
Rahoton ya ce wata kungiya mai tsananin kiyayya da musulmi ta shirya gudanar da
wata gagarumar zanga-zanga a yau a birnin, domin nuna kyama ga baki musamman
musulmi a birnin, kuma an shiya cewa za a rufe zanga-zangar ne a babban filin
shkata na birnin, inda musulmi suke gudanar da sallar idi a kowace.
Da dama daga cikin musulmin dai sun bayyana cewa wannan zanga-zangar ta yau
tana dauke da sakonni a gare su, daga ciki kuwa har da barazana gare su kan
gudanar da sallar idi da suke yi duk shekara, a kan haka sun fasa gudanar da
sallar saboda sdalilai na kare rayuwarsu.