IQNA

Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Harin Madina Da Kuma Qatif

20:02 - July 05, 2016
Lambar Labari: 3480584
Bangaren kasa da kasa, kungiyar Hizbullah ta yi Allawadai da kakakusar murya dangane da harun ta’addancin da aka kaddamar kan masallacin manzo da kuma yankin Qatif na gabashin Saudiyya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na tashar Alalam cewa, kungiyar Hizbullah ta yi tir da Allawadai da harin ta'addancin da takfiriyawa suka kaddamar a kusa da masallacin manzon Allah (SAW) a birnin Madina da kuma a yankin Qatif, tare da bayyana hakan a matsayin hakikanin akidar 'yan ta'addan Takfiriyya da kuma yadda suke kallon sauran musulmi.

Bayanin na Hizbullah ya kirayi kasashen da suke daukar nauyin 'yan ta'addan domin cimma manufofi na siyasa da cewa su dauki darasi.

Ita ma a nata bangaren jamhuriyar muslunci ta fitar da bayani na yin Allawadai da kakkausar murya dangane da hare-haren da aka kai jiya a kasar Saudiyya da hakan ya hada da masallacin manzon Allah (SAW).

kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ne ya sanar da hakan a daren jiya Litinin, inda ya ce abin da ya faru abin bakin ciki ne da yin Allawadai.

Ya kara da cewa tun kafin wannan lokacin jamhuriyar musulunci ta kirayi kasashen yankin da su a jiye duk wani batu na siyasa, su hada karfi da karfe wajen ganin an yaki hadarin ta'addanci da ke barazana ga kowa a yankin.

Ya ce sun yi Allawadai da harin da aka kaddamar a kusa da masallacin manzon Allah (SAW) da kakkausar murya, tare da bayyana hakana matsyin kai hari a kan addinin musulunci da musulmi baki daya, kamar yadda kuma ta yi Allawadai da harin da aka kai a jiya a masallacin mabiya mazhabar shi'a a yankin Qatif .

3512934

captcha