IQNA

Kasashen Da Suka Sanar Da Idi A Yau / Saudiyya Gobe

20:04 - July 05, 2016
Lambar Labari: 3480585
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin kasashe da suka hada da na yankin Balkan sun sanar da yau a matsayin ranar idin karamar salla.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yanar gizo na Aljazeeranet cewa, kasashe da dama za su gudanar da sallar idi a gobe, amma kasashen Turkiya, Rasha da Mauritaniya da na yankin Balkan sun gudanar da salla a yau.

Bayanbin ya ce wadannan kasashe sun gudanar da idin ne bisa bayanan da malaman kasashen mas bayar da fatawa suka fitar kan hakan.

Daga cikin kasashen da suka sanar da gobe a matsayin sallar idi kuwa akwai Saudiyya, Kuwait, Qatar, Yemen, Palastinu, Jordan, Masar, da Lebanon, Syria, Sudan, Tunisia, Indonesia, Malayzia, Thailand, Japan, UAE, Libya, da New Zealand da wasu kasashen latin Amurka.

Sai Iran, Oman, Morocco, Burnai, Pakistan, India, Bangaladesh, Siri Lanka da wasu kasashen Afirka sun ce gobe cikon watan Ramadan ne.

  1. 3512962

captcha