
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na nyanar gizo na Mir’at Bahrain cewa, a yau dukkanin limaman juma’a na kasar sun yi kira ga jama’a da su yi gangami a gaban masallatai domin nuna rashin amincewa da matakan hana su gudanar da iabada da iyalan gidan khalifa ke yi.
Limaman suka suka matakan da gidan sarautar al khalifa ke dauka na takura ma mabiya mazhabar Ahl;ul bait (AS) ya wuce iyaka, kuma dole ne daga yanzu komai ya dauke salon a canji.
Tun bayan da mahukuntan masarautar kama karya ta iyalan gidan khalifa ta fara daukar matakan zalunci da nuna kiyay a kn mabiya tafarkin ahlul bait a kasar, a kowace rana suna fitar da sabbin dokoki na nuna bangaranci a kan mabiya mazhabr ahlul bait wadanda su en amsu rinjaye a kasar.