IQNA

Harin Ta’addanci A Gefen Haramin Sayyid Muhammad (AS)

23:31 - July 08, 2016
Lambar Labari: 3480592
Bangaren kasa da kasa, ‘yan ta’addab Deash sun kaddamar da hari a gefen haramin Sayyid Muhammad dan Imam Hadi (AS) a unguwar Balad inda suka kasha mutane 35 wasu 65 suka jikkata.

Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, wasu gungun 'yan ta'adda sun farma hubbaren daya daga cikin jikokin Manzon Allah {s.a.w} a garin Balad da ke lardin Salahuddeen na kasar Iraki, inda suka kashe mutane akalla talatin da biyar tare da jikkata wasu da dama.

Majiyar tsaron Iraki ta sanar da cewa: Wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Da'ish masu kafirta musulmi sun kaddamar da wani mummunan harin ta'addanci a Hubbaren Sayyid Muhammad bin Ali Al-Hadi {a.s} wato dan jagoran shiriya na goma daga cikin shugabannin shiriya goma sha biyu na iyalan gidan manzon Allah tsarkaka {a.s} a yammacin jiya Alhamis da ke garin Balad a lardin Salahuddeen na kasar Iraki.

Yan ta'adda biyu sun tarwatsa kansu a kusa da kofar shiga harabar hubbaren a tsakanin 'yan shi'a da suke ziyara, yayin wasu gungun 'yan ta'addan suka bude wutan bindiga kan jama'a lamarin da ya kai ga shahadar mutane akalla 35 tare da jikkatan wasu fiye da sittin na daban.

Jami'an tsaron Iraki sun samu nasarar halaka da dama daga cikin 'yan ta'adda.

3513417

captcha