IQNA

An Sanar Daukar Matakai Na Tsaro A Cibiyoyin Musulmi A London

21:39 - July 09, 2016
Lambar Labari: 3480593
Bangaren kasa da kasa, jami'an tsaron kasar Birtaniya sun dauki tsauraran matakan tsaroa wasu cibiyoyin musulmi a birnin London fadar mulkin kasar.
Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar Indepent cewa, sakamakon bincike kan lamurra da suka danganci ta'addanci jami'an tsaro sun tsananata bincike a cibiyoyin muslunci a Totengham da Liton.

Bayanin ya ci gaba da cewa an dauki wannan matakin ne bayan da aka ga ana ajiye wasu ledoji da aka kunshe da ba a san abin da ke ciki ba.

Hakan kuwa sakamako ne na nuna kyamar musulmi da wasu ke yi a kasar da kuma nuna alamu na cutar da su, wanda hakan ya saka shakkua cikin zukatan musulmi kan manufar hakan.

Sai daga bisani bayan gudanar da bincike kan wasu daga cikin irin wannan kunshi da aka samu ana ajyewa a wasu cibiyoyin musulmi an samu wata hoda wadda ba za ta iya cutar da dan adam ba.

A cikin shekarar da ta gabata an samu cutar da musulmi har sau 326 a fadin kasar, wanda hakan ne nuni da cewa kyamar musulmi na ci gaba da karuwa a kasar fiye da kowane lokaci.

Wannan lamari dai ya fi shafar mata muulmi wadanda suke aka hijabi, wadanda ake saurin gane su daga shigarsu da kuma tufafin da suek sakawa.

3513576

captcha