IQNA

Mutanen Da Suka Rasu Sakamakon harin Najeriya Sun Kai 9

21:43 - July 09, 2016
Lambar Labari: 3480595
Bangaren kasa da kasa, sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallaci a cikin jahar Borno da ke arewa maso gabashin najeriya mutane 9 sun rasa rasa rayukansu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na aynar gizo na Fax News cewa, wani babban jami'in sojin Najeriya ya bayyana cewa, yan kungiyar boko haram sun kashe mutane tara a wani harin kunar baki a masallaci.

Majiyar Sojan Najeriya ta ce; Wani dan kunar bakin wake ya kashe mutane 6 a cikin masallacin garin Dambua da ke jahar Borno.

Kakakin sojan Najeriya, sani sman, ya sanar a yau juma'a cewa; An dakile harin farko da aka so kai wa a babban masallaci garin, sai dai dan kunar bakin wake na biyu ya tashi kansa a cikin wani karamin masallaci.

Kawo ya zuwa an tabbatar da mutuwar mutane tara.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin, sai dai kungiyar bokoharam ce aka sani da hari irin wannan.

Kafin wanann lokacin dai rundunar sojin kasar ta ce ta samu nasarar murkushe yan ta'addan a yankunan da suka addaba, amma a bin da ke faruwa yanzu ya sake sak mutane cikin wani hali.

3513516

captcha