IQNA

An Allawadai Da Farmakin Yahudawan A Kan Masallacin Aqsa

23:51 - July 10, 2016
Lambar Labari: 3480597
Bangaren kasa da kasa, an yi Allawadai da farmakin da yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’ayi ska kaddamar kan masallacin aqsa mai alfarma.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto dag shafin sadarwa na yanara gizo na Ina cewa, cibiyar da ke kula da harkokin masallacin Quds ta yi Allawadai da farmakin da yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’ayi ska kaddamar kan masallacin aqsa a cikin kwanakin nan.

Bayanin ya ce abin da yahudawan suka yi ya wuce dukkanin iyakoki, domin kuwa sun zarafin dukkanin addinai da aka safkar daga sama tare da keta huruminsu.

Hakan kuma bayanin ya kara da cewa, yin amfani da makamai da yahudawan suka yi wajen kai hari kan fararen hula palastionawa musamman ma mata, tare da hana dbban muslmi isa wurin salla awannan masallaci, ya saba wa dukkanin dokoki na majalisar dinkin duniya.

A karshen watan Ramadan ne yan sandan yahudawan Isra’ila suka dauki matakin hana palastina shiga birnin Quds da dama dukkanin yankunan da suke kusa, domin hana gudanar da ranar quds ta duniya.

3513979

captcha