IQNA

Mutanen Texas Sun Yi Gangami Domin Goyon Bayan Musulmi

23:53 - July 10, 2016
Lambar Labari: 3480598
Bangaren kasa da kasa, daruruwan mutanen a yankin Brain College Station a jahar Texas sn gudanar da wani da gangami domin nuna goyon bayansu ga musulmi.

Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na KBTX cewa, mutane da dama sun gudanar da gangamia jahar Texas domin nuna rashin amincewarsu da harbin da aka yi a kan masallaci na muslmi.

Wasu daga cikin wadanda suka shiga cikin gangamin sun bayyana cewa, babu wani dalili da zai sanya masu kyamar muslunci su yi harbi a kan wannan masallaci, domin kuwa shekara da shekaru musulmi suna gudanar da harkokinsu a wurin bas u taba tayar da hankalin wani ba.

Da dama daga cikin mutanen yankin da abin ya faru sun nuna rashin jin dadin su, tare da bayyana cewa haika wadabnda bas u son zaman lafiya a tsakanin a’ummar kasar ne suka yi wannan danyen aiki.

Babbar cibiyar da ke kula da harkokin msuulmi a yankin dai ta kirayi mahukunta da su bayar da kariya ga musolmi a yanki bayan abin da ya faru na kai farmaki da bindiga a kan masallata a wannan wuri.

Jahar Texas dai na daga cikin jahohin da musumi suke fuskantar matasala daga masu tsananin kiyayya da adinin muslunci, inda koa makon da ya gabata an lakada wani likta musulmi duka a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa masallaci.

3513852

captcha