IQNA

Cibiyar Azhar Ta Fito Ta Yi Allawadai Da Harin Yankin Karada Na Iraki

22:10 - July 11, 2016
Lambar Labari: 3480601
Bangaren kasa da kasa, daga karshe dai cibiyar Azahar ta fito ta yi Allawadai da harin da aka kai yankin karada na bagadaza.
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa tashar talabijin ta al'alam ta bayar da rahoton cewa, a yau cibiyar Azhar ta kasar Masar ta fitar da wani bayani, wanda a cikinda ta yi Allawadai da da harin ta'addancin da aka kai a yankin Karada da ke birnin Bagadaza a daren Lahadin makon da ya gabata, a lokcin da mutane suke hada-hada bayan buda baki.

Bayanin na Azhar ya ce wannan aiki ne na dabbanci da ba shi da wata alaka da addinin mulsunci balantana sunnar ma'aikai tare da yin kira ga sauran malaman addini da su mike wajen fadakar matasa irin hadarin da ke tatatre da wannan mummunar akida da ke yaduwa a tsakanin matasan musulmi.

Fitar da wannan bayani na Azhar dai ya zo ne bayan kakakusar sukar da shugaban kungiyar malaman sunnah a Iraki a Iraki Shekh Khalid Mulla ya yi ne, inda ya ce gum da bakin da Azhar ta yi kan harin Karada wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da ari uku abin kunya ne da ban takaici, kuma hakan zai kara karfafa gwaiwar 'yan ta'addan domin ci gaba da abin da suke yi.

3514174

captcha