
Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nilain cewa, Sheikh Muhammad Hashem Hakim daya daga cikin mambobin majalisar malaman kasar Sudan ya yi gargadi dangane da buga kur’ani da kure a wata madaba’anta.
Ya ce wannan madaba’anta ta samu izinin buga littafan addini ne mai lamba 26 daga cibiyar Azhar ta Masar a cikin shekara ta 2015, inda ta fara buga littafai a kasar tana yadawa.
Hakim ya kara da cewa kwafin kur’ani da wannan madabanta ta buga yana dauke da manyan kurakurai na bugu, inda babu aya ta 64 daga surat Al—imran, da kuma wasu shafuka 10 na kur’ani.
Ya kara da cewa wannan lamari yana da matukar hadari indai ahar a aka ci gab ada yada wannan kur’ania tsakanin mutane, domin kuwa bai cika ba, alhali mutane suna karanta shia matsayin cikakken kur’ani.