IQNA

Mutanen Bahrain Za Su Kawo Karshen Killace Ayatollah Isa Qasem

22:01 - July 13, 2016
Lambar Labari: 3480606
Bangaren kasa da kasa, mutanen kasar Bahrain sun shirya gudanar da wani gagarumin jerin gwano a gobe domin kawo karshen killacewar da ake yi Ayatollah Sheikh isa Qasem.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin alalam cewa, wannan gangami gamayyar matasan 14 ga Fabrairu ne suka kira shi.

Babbar manufar wanann gangami dai ita ce kawo karshen killace kauye Diraz da jami'an tsaron masarautar kasar ke yi, domin hana jama'a isa gidan Ayatollah Sheikh Isa Qasem

Bayanin ya ci gaba da cewa irin matakan da mahukuntan kama karya na wannan kasa suke dauka a kan wanann bababn malami mafi tasiri a tsakanin al'ummar kasar ya wuce dukkanin iyaka.

Ayatollah Isa Qasem dai mahukuntan mulkin kama karya na masautar iyalan gidan Khalifa ne suka sanar da janye masa izinin zama dan kasa, lamarin da ya harzuka jama'a tare da daukar matakin tunkarar wannan zalunci maras misiltuwa.

Matasan gungun 14 ga Fabrairu sun kira wannan gangami da jerin gwano da za su gudanar a gobe da jerin gwanon arbain na Imam Hussain (AS) a yankuna na kasar.

3514902

captcha