Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga
shafin sadarwa na yanar gizo na Alanba ta kasar Kuwait cewa, a jiya ne aka fara
gudanar da wata gasar hardar kur'ani mai tsarki wadda ta hada malamai da kuma
dalibai a karkashin jagorancin cibiyar Al-rahma.
Ali Rashid shi ne wakilin cibiyar ta Al-rahma wanda ya kasance a wajen gudanar da wanann gasa, ya bayyana cewa bababr manufarsu ita ce yada koyarwar kur'ani mai tsarki, da kuma yin amfani da hakan wajen taimaka ma marassa karfi.
Ya ce hakika isar da sakon kur'ani mai tsarki da kuma koyar da ilmominsa shi ne babbar manufarsu, inda hakan yake a matsayin wani aiki na wajibi a kan musulmi su isar da sakon da ke cikin kur'ani ga al'ummomi.
Shirin dai ya kebanci mabiya addinin muslunci ne, amma hatta wadanda ba musumi ba suna da damar da za su iya zuwa wurin domin kallo, ko kuma gabatar da tambayoyinsu kana bin da ya shige musu duhu.
Wannan shiri dai ya samu karbuwa daga musulmi da dama a kasashen duniya daban-daban, kuma ana ci gaba da kara bunkasa yawan makarantu da cibiyoyi na ilimin kur'ani a karkashin wanann cibiya.
Cibiyar Al-rahma wadda take da alaka da wata cibiyar jin kai a kasar Kuwait, tana da makarantu da cibiyoyin kur'ani a kasashen duniya, kamar yadda a wannan kasa tana da dalibai fiye da 1000 da suke daukar ilmomin kur'ani mai tsarki.