IQNA

Gangamin Allawadai Da Tashin Hankali Da Sunan Addini

22:05 - July 13, 2016
Lambar Labari: 3480608
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani babban gangami wanda ya hada kungiyoyi da cibiyoyin musulunci a jahar New Jersey ta kasar Amurka domin yin Allawadai da tashin hankali da sunan addini.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na GMNews cewa, tashin hankali da ta'addanci baya wakiltar wani addini daga cikin addinai da aka safkar daga sama.

Bayanin ya ce addinin muslunci addini ne na zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai, kuma duk wanda yake ta'addanci da cutar da yan adam da sunan muslunci baya wakiltar musulmi balantana addinin muslunci.

Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa musulmin New Jersey ba za su taba yan ta'adda su kawo karshen fahimta da kaunar juna da ke tsakaninsu da sauran mabiya addinai a wanann jahar ba.

Kungiyar dalibai ta Ahlul bait AS) da kuma cibiyar Alhuda, gami da cibiyar Al-tauhid da sauran cibiyoyin musulmi suna daga cikin wadanda suka hada wanann gangami.

Babbar cibiyar musulmin wannan jaha dai tana gudanar da ayyukan jin kai da dam a cikin yankunan kasar Amurka da ma wasu kasashen duniya, ta hanyar tallafawa masu fama da matsaloli na rayuwa da marassa galihu, da masu fama da yunwa.

Wasu daga cikin mabiya addinin kirista suna shiga ana gudanar da irin wadannan ayyuka tare da su, kasantuwar aiki ne na jin kan dan adam da musulmin suke gudanarwa ba tare da banbanta addinin mutum da yake butar taimako ba.

Daga karshe bayanin ya yi Allawadai da kakkausar murya dangane da hare-haren ta'addancin da aka kai a Turkiya, da Iraki, da kuam Bangaladesh da sauransu.

captcha