IQNA

Zaman Mako-Mako Na Tadabbur A Cikin Kur’ani A Kuwait

21:12 - July 14, 2016
Lambar Labari: 3480609
Bangaren kasa sa kasa, ana gudanar da wani zama mai taken tunani kan kur’ani a Husainiyar Mahdawiyyah a Kuwait.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar QAF cewa, wanna zama yana mayar da hankali ne ga kiyaye kaidoji na karatu wato tajwidi da kuma hardar kur’ani mai tsarki.

Haka nan kuma ana gudanar da zaman a kowace ranar Talata daga karfe 9 zuwa 10 na dare, tare da halartar mutane da dama wadanda suke gabatar da kartu da kuma harda gwargwadon abin da suka hardace, masu shekaru sama da 14 ne kawai suke halartar wurin.

Yusuf Hujairat na daga cikin wadanda suke koyar da karatu da harda da kuma kaidojin karatu a wurin.

3514802

captcha