IQNA

Kasashen Musulmi Da Na Larabawa Suna Allawadai Da Harin Nice Faransa

23:39 - July 15, 2016
Lambar Labari: 3480613
Bangaren kasa da kasa, kasashen musulmi da na larabwa suna ci gaba da mayar da martini kan harin da aka kai a birnin Nice na kasar faransa a jiya.

Kamfanin dillancin labaranIqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yada labarai na yanar gizo na Al-ain cewa, kasashen larabawa na a sahun gaba wajen yin allawadai da harin NIce da ya halka mutane kimanin 84 tare da kira kan a hada kai domin yaki da ta'adanci.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Ijamhuriyar muslunci ya ce abun allawai ne wannan harin kuma Iran tana jajatawa al'ummar faransa.

Tuni dai shugaban majalisar dokokin faransa ya jinkirata ziyara daya shirya kawo wa a makon mai zuwa anan jamhuriyar muslunci.

Wannan dai na zuwa a daidai lokacin da binciken ya nuna cewa wani dan kasar ne ta Faransa dan asalin kasar Tunisiya ya kai harin.

Sakamakon harin da wani mutum dan asalin kasar tunisia ya kai a kan mutane masu shagulgulan ranar 'yancin kasar Faransa a birnin Nice a cikin daren jiya akalla mutane da dama sun rasa rayukansu.

Mutumin da ya kai harin ya yi amfani da babbar mota wajen kutsawa a cikin dubban masu taron, inda ya yi ta taka su kuma yana harbi da wata karamar bindiga da ke hannunsa, kafin daga bisani jami'an 'yan sanda su harbe shi kuma suka kashe shi.

3515132


captcha