
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Oman cewa, ana gudanar da wannan gasa nea karkashin shirin ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar.
Wannan gadsa wadda ta kebanci mata zalla ana gudnar da ita ne tare da halartar masu gudanar da ita daga yankunan badbad da kuma Sama’il gami da wasu yankunan da ke gefen birnin maskat fadar mulkin kasar.
Hannan Bint Hamid Al-sabiyah wadda it ace babbr mai jagorantar shirinta bayyana cewa, yanzu haka dai akwai mata fiye da 100 da suka karawa da juna a wannan gasa.
Ta kara da cewa, bisa la’akari da cewa gasar ta kunshi bangarori na harda da kuma tajwidi, wannan ya sanya kwamitin alkalan gasar sun kunshi na dukaknin bangarorin da ake gudanar da gasar.