IQNA

A Lokacin Da Mai Kyamar Muslunci Ke Buga Misali Da Kur’ani

23:44 - July 16, 2016
Lambar Labari: 3480616
Bangaren kasa da kasa, masu mu’amala da shafukan yanar gizo sun saka wani faifan bidiyo na firayi ministan Ingila Theresa May tana ambaton wata aya daga kur’ani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Uyon Khalij cewa, a lokacin da take gabtar da wani jawabi sabuwar firayi ministan Birtaniya Theresa May ta ambaci wata ayar kur’ani da ke nuna cewa muslunci yana girmama dan adam.

Ta karanta aya ta 13 daga surat Hujrat da ke yin ishara da cewa, "Yak u mutane ne mun hallice ku maza da mata, muka sanya ku al’ummomi da kabilu domin ku san juna, wanda yafi a wurin Allah shi ne wanda ya fi tsoron Allah madaukakin sarki”.

Haka nan kuma ta karanta aya ta 256 a cikin surat Bakara da ke yin ishara da cewa, "Babu tilascia cikin addini, shiriya ta bayyana daga bata, duk wanda ya kafurce ma datugu to hakika ya yi riko da iggiya mai tabbaci har zuwa karshen aya.

Wannan mata ta bayyana haka ne a lokacin da take kokarin ta bayyana cewa muslunci yana kare hakkin bil adama, amma babban a bin da ya bayar da mamamki shi ne yadda ta kasance a cikin shekara ta 2015 tana bayyana kiyayayrta a fili a kan addinin muslunci da kuma kyamar musulmi.

Bayanin nata da take gabatarwa a gaban daliban jami’a ya sanya kowa ya yi shiru saboda matukar mamaki dangane da yadda take kafa dalili da kur’ani kan cewa muslnci addinin zaman lafiya ne, sabanin ra’ayinta da aka santa da shi a lokutan baya.

3515249

captcha