IQNA

Mutane 900 Sun Muslunta A Kasar India

23:48 - July 17, 2016
Lambar Labari: 3480620
Bangaren kasa da kasa, cibiyoyin Subha da Tarbiya sun muslunctar da mutane 900 a cikin shekara ta 2015 da ta gabata a Kirala.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sunday Standard cewa, Ali Kuya daga daga cikin shgabannin ciboyoyin muslunci a yankin ya bayyana cewa, cibiyoyin sun muslunctar da mutane Subha mutane 300 sai kuma Tarbiya mutane 600 duk a cikin shekara ta 2015.

Dukkanin abin da wadannan cibiyoyi suke yi suna gudanar da shi ne tare da hadin gwiwa da jami’an ‘yan sanda na yankin, tare da karyata bayanan da ke danganta muuslmin wannan yankin da kungiyar yan ta’adda ta Daesh.

A cikin shekara ta 2006 kimanin mutane 2667 ne suka muslunta a cikin wannan yankin na Kirala.

Haka nan kuma kimanin kasha 27 cikin dari na dukkanin mutanen yankin mabiya addinin muslunci ne, wato kimanin mutane miliyan daya kenan.

A wasu yankunan lardin Kirala kamar su Kuchin Kalikt adadin muslmi ya kai kimanin kasha 95 cikin dari na dukkanin mutanen yankin.

3515505

captcha