
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin Alwasat cewa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasa baki daya a Libyaa yankin Zuwarah a babban dakin taro na Farhat Halab.
Jauhar Sharef shugaban kwamitin gasar ya bayyana cewa wannan gasa za ta ci gaba da gudana a garuruwa daban-daban na kasar Libya har zuwa tsawon kwanaki 5 a nan gaba.
Sharef ya kara da cewa yanzu haka akwai matasa da suke gabatar da gasar da suka fito daga yankunan daban-daban a bangarorin gasar, da hakan ya hada da harda, karatu da kuma bangaren tajwidi.
Babbar manufar wannan gasa dai wadda ake gudanarwa karo an ashirin da biyar ita kara karfafa matasa wajen mayar da haknaki ga harkokin kur'ani mai tsarki.
Dukkanin bangarorin da ake gudanar da gasar za a fitar da wadanda suka fi nuna kwazo a mataki na daya da na biyu zuwa na uku, inda za a bas u kyautuka na musamman domin kara karfafa gwiwarsu wajen ci gaba mayar da hankali ga lamurran kur'ani mai tsarki.