IQNA

Kungiyar Daesh Ta Dauki Alhakin Harin Da Wani Ya Kai A Cikin Jirgin Kasa A Jamus

23:36 - July 19, 2016
Lambar Labari: 3480628
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar 'yan ta'adda ta ISI ta sanar da cewa ita ce take da alhakin kaddamar da hari kan matafiya a cikin jirgin kasa a kasar Jamus.

Kamfanin dillancin labaran Iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, A cikin bayanin da kungiyar ta bayar a shafin da take bayar da sanarwa ta hanyar yanar gizo ta bayyana cewa, mutumin da ya kai hari da gatari da wukake a kan matafiya a cikin jirgin kasa a yankin Wurzburg na kasar Jamus, mamba ne a kungiyar.

A jiya ne matashin mai shekaru 17 da haihuwa dan asalin kasar Afghanistan ya kaddamar da harin, inda ya yi ta daba wukake da sara da gatari a kan matafiya a cikin jirgin kasa a Wurzburg da ke Jamus, ya dai jikkata mutane 3, daya daga cikinsu kuma yana cikin mawuyacin hali.

Jami'an tsaron kasar ta Jamus da ke gudanar da bincike kan lamarin, sun sun samu wasu totoci na kungiyar Daesh a masafkinsa, wanda hakan ke nuna alaun cewa yana da alaka da wannan kungiya.

3516281

captcha